Juventus za ta sake daukar Pogba, Dembele zai koma Liverpool


Newcastle United na son daukar dan wasan Napoli mai taka leda a Senegal, Kalidou Koulibaly daya daga cikin 'yan wasan da za ta dauka. (Football Insider)


Newcastle za ta fara da daukar dan wasan Burnley, James Tarkowski da kuma Jesse Lingard na Manchester United wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana. (Sunday Telegraph)


Haka kuma Newcastle na fatan daukar dan wasan Paris St-Germain, Mauro Icardi koda yake Tottenham da kuma Juventus na son yin zawarcin dan wasan mai shekara 28. (Calciomercato, via Mail on Sunday)


Newcastle United za ta kori kocinta, Steve Bruce a makon gobe. (Sunday Mirror)


TALLA


Tsohon mai kungiyar Newcastle, Mike Ashley na sha'awar sayen Derby County mai buga Championship wadda kef ama da matsin tattalin arziki. (Sunday Mirror)


Watakila Juventus tana da damar sake daukar Paul Pogba, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana Manchester United, kafin nan idan za su iya sayar da fitattun 'yan wasa domin samun kudin daukarsa. (La Gazzetta dello Sport, via Football Italia)


Pogba ya matsar da kwalbar barasa daga gabansa

Kasuwar 'yan wasa: Makomar Pogba, Haaland, Olmo, Lingard, Bailly, Tchouameni

West Ham 1-2 Man Utd: Cristiano Ronaldo da Jesse Lingard sun ci kwallo

Liverpool na Shirin daukar Ousmane Dembele a karshen kakar bana idan kwantiraginsa ya karkare da Barcelona. (Teamtalk)


Leeds United tana da tabbacin cewar Kalvin Phillips zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar kafin karshen shekarar nan, bayan da suke kan tattaunawa. (Football Insider)


Manchester United na son fara tattaunawa da Harry Maguire domin tsawaita kwantiraginsa a Old Trafford. (Sunday Mirror)


Inter Milan na bibiyar dan wasan Arsenal, Alexandre Lacazette da na Real Madrid, Luka Jovic wadanda take son dauka a watan Janairu. (La Gazzetta dello Sport, via Football Italia)


Sevilla na auna yadda za ta sayo dan kwallon Blackburn Rovers, Ben Brereton, bayan da ake alakanta dan wasanta, Youssef En-Nesyri da cewar zai koma taka leda Arsenal ko kuma Tottenham. (Teamtalk)


--------------------------------------------------

Inda aka samo labari: BBC

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.