Wani rahoto da gidan Radio Dala FM dake Kano ya kawo ya bayyana cewa wani kamfani ya kai ƙarar jarumar Kannywood Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya, zuwa gaban babbar kotun jihar Kano, wacce ke Ungoggo, kan zargin cinye zunzurutun kuɗi har naira miliyan daya da dubu dari uku da aka bata domin daukar bidiyon rawa, amma ta saɓa alkawari.
Rahoton ya bayyana cewa jarumar ta zo gurin bikin, har an fara daukar bidiyon, sai kuma ta gudu ba ta dawo ba, inda hakan yasa kamfanin ke buƙatar kotu ta sa ta dawo musu da kuɗin su, kana ta biya su naira miliyan goma.