Alomomin Soyayya


♥♥ALAMOMIN SO♥♥

Akwai alamomin dake fitar da so, masu tarin yawa suke bayyana soyayya ga kadan  daga ciki.


1. ♥KUNYA♥

da zarar soyayya ta fara shiga ko da ba a yi furuci ba sai kunya ta shiga tsakani, sai aga masoyan a junansu suna jin kunyar juna.


2. ♥YAWAN KALLO♥

wannan alamace ta soyayya,misali ta hanyar yawan satar kallo, idan masoyi yana kallon a bin son shi da ya waiga sun hada ido xai kawar da kansa.


3. ♥FADUWAR GABA♥

a lokacin da soyayya ta fara shiga xuciyatr saurayi ko budurwa xa ka samu da zarar sun hango juna kowa sai gabansa ya fadi


Koma Karanta:  Soyayya: Karanta Abubuwanda suke Da Amfani Gareka

4. ♥YAWAN AMBATO♥

matukar soyayyar saurayi ta kafu a zutciyar budurwa ko ta budurwa ta shiga ran saurayi xaka samu yana yawan kawo labarin wanda yake so din ako yaushe, kuma duk inda ya ji an fara labarin wanda yake son xa kaga ya nutsu yana sauraro.


5. ♥TAUSAYI♥

soyayya musamman ta gaskiya tana tare da tausayi. Kuma sau tari zakaga masoyi ko masoyiya suna matukar tausayi ga junansu har hakan na haifar da damuwa ko saurin kuka musamman mata. Assalamu Alaikum. Barka da hawa online!!!


Abubuwanda Babu a Soyayya

  • A soyayya babu kunya.
  • A soyayya babu tsoro.
  • A soyayya babu cin amana.
  • A soyayya babu karami babu babba.
  • A soyayya babu attajiri babu talaka.
  • A soyayya babu jan aji.
  • A soyayya babu hanzari.


Abubuwan Da Soyayya Kan Haifar

  • A soyayya ake samun yarda.
  • A soyayya ake jin dadin rayuwa.
  • A soyayya ake samun farin ciki.
  • A soyayya ake shiga kunci.
  • A soyayya ake abota.
  • A soyayya ake samun karamci.
  • A soyayya muke rayuwa.
  • A soyayya muke farin ciki.
  • A soyayya muke aure.
  • A soyayya muke samun ‘ya’ya.
  • A soyayya muke furta kalamai.
  • A soyayya aka san farin ciki.
  • A soyayya aka san bakn ciki.
  • A soyayya aka san aure.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.